1 Sarakuna 17:17-24
17
Ana nan sai ɗan matan, wato, gwauruwan nan ya fara ciwo. Ciwon ya ƙara muni, daga ƙarshe sai ya daina numfashi.
18
Sai ta ce wa Iliya, “Mutumin Allah, yaya haka? Ka zo ne domin ka nuna wa Allah zunubaina, ka kuma jawo mutuwar ɗana?”
19
Iliya ya ce, “Ki miƙa mini ɗanki.” Sai ya ɗauke shi daga hannuwanta, ya kai shi ɗakin sama inda yake zama, ya kwantar da shi a gadonsa.
20
Sa’an nan ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wannan masifa a kan gwauruwan nan? Kai ka ce in zauna tare da ita, ga shi yanzu ɗanta ya mutu.”
21
Sai ya kwanta, ya miƙe kansa a kan yaron sau uku, ya kuma yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka mai da ran yaron nan!”
22
Ubangiji kuwa ya ji kukan Iliya, sai ran yaron ya dawo masa, ya kuma rayu.
23
Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga ɗakin sama zuwa cikin gida. Ya ba da shi ga mahaifiyarsa, ya ce, “Duba, ɗanki yana da rai!”
24
Sai matar ta ce wa Iliya, “Yanzu na san cewa kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuma yana magana ta wurinka.”
Settings