1 Sarakuna 17:1-7
1
To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.”
2
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce,
3
“Ka bar nan, ka nufi wajajen gabas, ka ɓuya a Rafin Kerit, gabas da Urdun.
4
Za ka sha daga rafin, zan kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”
5
Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can.
6
Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin.
7
Ana nan sai rafin ya bushe saboda ba a yi ruwan sama a ƙasar ba.
Settings