1 Sarakuna 11:35-42
35
Zan ɗauke masarautar daga hannuwan ɗansa ne, in ba ka kabilu goma.
36
Zan ba da ɗaya ga ɗansa don kullum Dawuda bawana yă kasance da fitila a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa Sunana.
37
Amma fa, ga kai, zan ɗauke ka, za ka kuwa yi mulki bisa dukan abin da zuciyarka take so; za ka zama sarki a bisa Isra’ila.
38
In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka.
39
Zan ƙasƙantar da zuriyar Dawuda saboda wannan, amma ba har abada ba.’ ”
40
Solomon ya yi ƙoƙari yă kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tsere zuwa Masar, zuwa wurin sarki Shishak, ya zauna a can sai bayan mutuwar Solomon.
41
Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, da dukan abubuwan da ya yi, da hikimar da ya nuna, an rubuta su a littafin tarihin Solomon.
42
Solomon ya yi mulki a Urushalima, a bisa dukan Isra’ila, shekaru arba’in.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings