Skip to content
1 Korintiyawa 6:1-11

1 Korintiyawa 6:1-11

1
In wani a cikinku yana da damuwa da wani, don me zai kai ƙara a gaban marasa bi, maimakon yă kai ƙara a gaban tsarkaka?
2
Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan.
3
Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba? Balle al’amuran da suka shafi duniyan nan!
4
Saboda haka, in kuna da damuwa game da irin waɗannan al’amura, sai ku naɗa alƙalai ko cikin waɗanda ba kome ba ne a ikkilisiya!
5
Na faɗi haka ne don ku ji kunya. Ashe, ba za a iya samun wani a cikinku mai hikima wanda zai iya sasanta tsakanin masu bi ba?
6
Me zai sa ɗan’uwa yă kai ƙarar ɗan’uwa, a gaban marasa bi?
7
Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku?
8
Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga ’yan’uwanku ne kuke yi wannan.
9
Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu,
10
ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.
11
Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options