1 Korintiyawa 16:15-18
15
Kun san cewa iyalin gidan Istifanas ne suka fara tuba a Akayya. Sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. Ina roƙonku ’yan’uwa,
16
ku ba da kanku ga irin waɗannan, ga kuma kowa da ya haɗa hannu a aikin, yana kuma faman a cikinsa.
17
Na yi farin ciki da isowar Istifanas, Fortunatus da Akaikus, domin sun biya bukatar da ba ku iya biya ba.
18
Gama sun wartsake ruhuna da kuma naku. Ya kamata ku girmama irin waɗannan mutane.
Settings