1 Korintiyawa 16:19-24
19
Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa. Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu.
20
Dukan ’yan’uwa a nan suna gaisuwa. Ku gai da juna da sumba mai tsarki.
21
Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna.
22
Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji!
23
Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku.
24
Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin.
Settings