Skip to content
1 Korintiyawa 15:12-28

1 Korintiyawa 15:12-28

12
Amma in ana wa’azi cewa Kiristi ya tashi daga matattu, yaya waɗansu a cikinku suke cewa babu tashin matattu?
13
In babu tashin matattu, to, ba a tā da Kiristi ma ba ke nan.
14
In ba a tashe Kiristi ba kuwa, ai, wa’azinmu, da bangaskiyarku banza ne.
15
Sai ma ya zama mun zama masu ba da shaidar ƙarya game da Allah ke nan, domin mun shaida game da Allah cewa ya tashe Kiristi daga matattu. Bai tashe Kiristi ba ke nan, in lalle ba a tā da matattu.
16
Gama in ba a tā da matattu ba, to, Kiristi ma ba a tashe shi ba ke nan.
17
In kuwa ba a tashe Kiristi ba, bangaskiyarku a banza take, ya zama har yanzu kuna cikin zunubanku ke nan.
18
Ashe, waɗanda suka yi barci a cikin Kiristi ma sun hallaka ke nan.
19
In a wannan rayuwar ce kaɗai muke da bege cikin Kiristi, mun zama abin tausayi fiye da dukan mutane.
20
Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci.
21
Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum.
22
Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi.
23
Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa.
24
Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko.
25
Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.
26
Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa.
27
Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi.
28
Sa’ad da ya yi haka, sa’an nan Ɗan kansa yă koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yă zama kome da kome.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options