1 Tarihi 24:20-31
20
Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.
21
Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.
22
Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat.
23
’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
24
Ɗan Uzziyel shi ne, Mika; daga ’ya’yan Mika maza, Shamir.
25
Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.
26
’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi. Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno.
27
’Ya’yan Merari su ne, daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.
28
Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza.
29
Daga Kish, ɗan Kish shi ne, Yerameyel.
30
Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu.
31
Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.
Settings