1 Tarihi 20:1-3
1
Da bazara, a lokacin da sarakuna kan tafi yaƙi, Yowab ya jagorance mayaƙa. Ya lalatar da ƙasar Ammonawa ya kuma tafi Rabba ya yi mata kwanto, amma Dawuda ya zauna a Urushalima. Yowab ya yaƙi Rabba, ya kuma bar ta kango.
2
Dawuda ya ɗauki rawani daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti na zinariya, aka kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, sai Dawuda kuwa ya sa a kansa. Ya kuma kwashi ganima mai yawa daga birnin
3
ya kuma fitar da mutanen da suke can, ya sa su aiki da zartuna da makamai masu kaifi da kuma gatura. Dawuda ya yi haka da dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da mayaƙansa gaba ɗaya suka koma Urushalima.
Settings