Skip to content
1 Tarihi 17:4-14

1 Tarihi 17:4-14

4
“Ka tafi ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ba kai ba ne za ka gida mini gidan da zan zauna a ciki.
5
Ban taɓa zama a gida daga ranar da na fito da Isra’ila daga Masar ba har wa yau. Na yi ta yawo daga gefen da aka kafa tenti zuwa wani, daga wannan wuri zuwa wancan.
6
Duk inda na tafi tare da Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani daga cikin shugabanninsu waɗanda na umarta su yi kiwon mutanena, “Don me ba ku gida mini gidan al’ul ba?” ’
7
“Yanzu, ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauke ka daga makiyaya da kuma daga bin garke, don ka zama mai mulki a bisa mutanena Isra’ila.
8
Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya.
9
Zan kuma tanada wuri domin mutanena Isra’ila, zan kuma kafa su saboda za su kasance da gidan kansu ba kuwa za a ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zaluntar su ba, yadda suka yi da farko
10
da kuma suka yi tun lokacin da na sa shugabanni a bisa mutanen Isra’ila. Zan rinjaye dukan abokan gābanka. “ ‘Na furta maka cewa Ubangiji zai gina maka gida,
11
sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin ’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka.
12
Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada.
13
Zan zama Ubansa, zai kuma zama ɗana. Ba zan taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi, kamar yadda na ɗauke ta daga wanda ya riga ka ba.
14
Zan sa shi a bisa gidana da mulkina har abada; kujerar sarautarsa za tă kahu har abada.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options