1 Tarihi 13:12-14
12
Dawuda ya ji tsoron Allah a wannan rana ya kuma yi tambaya, “Yaya zan taɓa kawo akwatin alkawarin Allah gare ni?”
13
Don haka bai ɗauki akwatin alkawarin ya kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka, ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat.
14
Akwatin Alkawarin Allah ya zauna tare da iyalin Obed-Edom a gidansa wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkaci gidan Obed-Edom da kome da yake da shi.
Settings