1 Tarihi 14:1-7
1
To, fa, Hiram sarkin Taya ya aika da ’yan aika zuwa wurin Dawuda, tare da gumaguman al’ul, maginan duwatsu da kafintoci, don su gina wa Dawuda fada.
2
Dawuda kuwa ya san cewa Ubangiji ya kafa shi a matsayin sarki a bisa Isra’ila kuma cewa an ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa Isra’ila.
3
A Urushalima, Dawuda ya ƙara auren waɗansu mata, ya kuma zama mahaifin ƙarin ’ya’yan maza da mata.
4
Ga sunayen yaran da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,
5
Ibhar, Elishuwa, Elfelet,
6
Noga, Nefeg, Yafiya,
7
Elishama, Beyeliyada da Elifelet.
Settings