Skip to content
1 Tarihi 13:1-4

1 Tarihi 13:1-4

1
Sai Dawuda ya tattauna da kowane ɗaya daga cikin shugabanninsa, shugabannin sojoji na dubu-dubu da na ɗari-ɗari.
2
Sa’an nan ya ce wa dukan taron Isra’ila, “In ya yi muku kyau kuma in nufin Ubangiji Allahnmu ne, bari mu aika da saƙo nesa da kuma ko’ina zuwa ga sauran ’yan’uwanmu a duk iyakokin Isra’ila, da kuma zuwa ga firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a garuruwansu da makiyayansu, su zo wurinmu.
3
Bari mu ɗauko akwatin alkawarin Allahnmu mu kawo wurinmu, gama ba mu neme shi a lokacin mulkin Shawulu ba.”
4
Dukan taron jama’a suka yarda su yi haka, domin ya yi daidai ga dukan mutane.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options