Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Virtue

4 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.

  2. Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”

  3. A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.

  4. Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani;