Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Turtle Dove: Burnt offering of
Ayoyi game da Burnt offering of
“ ‘In hadaya ga Ubangiji ɗin, hadaya ta ƙonawa ta tsuntsaye ce, zai miƙa kurciya ko ’yar tattabara.
Firist zai kawo ta bagade, yă murɗe wuyan tsuntsun yă ƙone shi a kan bagade; zai tsiyaye jininsa tsuntsun a gefen bagaden.
Amma zai ɗauki kayan cikin tsuntsun da gashin yă zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka.
Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, yă ƙone shi. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.