Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rizpah: Guards the bodies of her sons hanged by command of David

4 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Guards the bodies of her sons hanged by command of David

  1. Amma sarki ya ɗauki Armoni da Mefiboshet, ’ya’ya biyu maza waɗanda Rizfa ’yar Aiya ta haifa wa Shawulu, tare da ’ya’ya maza biyar na Merab ’yar Shawulu, waɗanda ta haifa wa Adriyel ɗan Barzillai, mutumin Mehola.

  2. Ya ba da su ga Gibeyonawa, waɗanda suka kashe su, suka kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji. Dukan bakwai ɗin an kashe su gaba ɗaya; an kashe su a farkon kwanankin girbi, daidai lokacin fara girbin sha’ir.

  3. Rizfa ’yar Aiya ta ɗauki tsumma ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutse. Tun daga farkon girbi har ruwa damina ya sauko a kan gawawwakin, ba tă yarda tsuntsayen sama su taɓa su da rana ko mugayen namun jeji da dare ba.

  4. Da aka gaya wa Dawuda abin da Rizfa ’yar Aiya ƙwarƙwaran Shawulu ta yi,