Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ophrah: 2. A city in Manasseh, home of Gideon

5 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da 2. A city in Manasseh, home of Gideon

  1. Sai mala’ikan Ubangiji ya zo ya zauna a ƙarƙashin itacen oak a Ofra na Yowash mutumin Abiyezer, inda ɗansa Gideyon yake sussukar alkama a wurin matsin inabi don yă ɓoye daga Midiyawa.

  2. Saboda haka Gideyon ya gina wa Ubangiji bagade a can, ya kuma kira shi, Ubangiji Salama ne. Har wa yau bagaden yana a Ofra ta mutanen Abiyezer.

  3. Gideyon ya efod da zinariyar, wanda ya ajiye a Ofra, garinsa. Dukan Isra’ila suka shiga yin karuwanci ta wurin yin sujada a can, ya kuwa zama wa Gideyon da dukan iyalinsa tarko.

  4. Gideyon ɗan Yowash ya rasu da kyakkyawan tsufa aka kuma binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa a Ofra na mutanen Abiyezer.

  5. Sai ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra kuma a dutse guda ya kashe ’yan’uwansa, ’ya’yan Yerub-Ba’al. Amma Yotam, autan ɗan Yerub-Ba’al ya tsira ta wurin ɓuya.