Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Meditation

42 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka.

  2. Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba.

  3. Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna, bawanka zai yi tunani a kan ƙa’idodinka.

  4. Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka.

  5. Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka.

  6. Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka.

  7. Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka.

  8. Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini.

  9. Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni.

  10. Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka.

  11. Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka.

  12. Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah! Yawansu ba su da iyaka!

  13. A ce zan iya ƙirgansu, za su fi yashin teku yawa. Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.

  14. Na tuna da kwanakin baya na yi tunani a kan dukan ayyukanka na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.

  15. Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa.

  16. Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka.

  17. Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka.