Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Lamb: Offering of

10 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Offering of

  1. “Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya.

  2. Ka miƙa ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma.

  3. Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.

  4. Ka miƙa ɗaya ragon da yamma, tare da hadaya ta gari da hadaya ta sha kamar aka yi ta safe, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  5. Ka gaya musu, ‘Ga hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, da za ku miƙa wa Ubangiji, raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya, marasa lahani.

  6. A miƙa rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma,

  7. tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau.

  8. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  9. Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki.

  10. Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa shi da yamma, tare irin hadaya ta lallausan gari, da hadaya ta sha da ka yi da safe. Wannan hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.