Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Groves

9 ayoyi · 19 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimi na biyu daga garken mahaifinka, wannan mai shekara bakwai. Ka rushe bagaden mahaifinka na Ba’al ka sare ginshiƙin Ashera kusa da ita.

  2. Sa’an nan ka gina bagade irin da ya dace wa Ubangiji Allahnka a kan wannan tudu. Ka yi amfani da itacen katakon ginshiƙin Ashera da ka sare, ka miƙa bijiman nan biyu hadaya ta ƙonawa.”

  3. Saboda haka Gideyon ya ɗebi bayinsa bakwai ya yi yadda Ubangiji ya ce masa. Amma saboda yana tsoron iyalinsa da mutanen gari, ya yi haka da dare a maimako da rana.

  4. Da safe sa’ad da mutanen garin suka tashi, sai suka tarar an rushe bagaden Ba’al, tare da ginshiƙin Ashera da yake kusa da shi, duk an sare, bijimi na biyu kuma aka miƙa hadaya a kan sabon bagaden!

  5. Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada.

  6. Ya gina bagadai a haikalin Ubangiji, wurin da Ubangiji ya ce, “A Urushalima ne zan sa Sunana.”

  7. Cikin filaye biyu na haikalin Ubangiji kuwa, ya gina bagadai na dukan rundunan taurari.

  8. Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

  9. Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.