Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Frankincense: Commerce in
Ayoyi game da Commerce in
“Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu
kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi;
kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane.