Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Forests

3 ayoyi · 22 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.”

  2. Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.”

  3. Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan, “Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir.