Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Evidence

9 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku, za a iya kashe mutum, amma ba za a iya kashe mutum bisa ga shaida mutum guda ba.

  2. Hannuwan shaidun ne za su zama na farko a kisan wanda ake zargin, sa’an nan hannuwan dukan mutane. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  3. Shaidar mutum guda ba tă isa a tabbatar cewa mutum yana da laifi game da laifin da ake tuhumarsa ba, ko kuwa a kan wani laifin da ake zaginsa da aikata ba. Dole a tabbata da batun ta bakin shaidu biyu, ko uku.

  4. In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi,

  5. dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.

  6. Dole alƙalan su yi bincike sosai, in kuma aka tabbatar mai ba da shaida maƙaryaci ne, yana ba da shaidar zur a kan ɗan’uwansa ne,

  7. to, sai a yi da shi yadda ya yi niyya yă yi da ɗan’uwansa. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  8. Sauran mutane za su ji wannan su kuma ji tsoro, ba kuwa za a ƙara yin irin wannan mugun abu a cikinku ba.

  9. Kada ku ji tausayi, rai yă zama a maimakon rai, ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa.