Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Character of the Wicked: Enticing to evil
Ayoyi game da Enticing to evil
Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.
In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;
mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;
ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”