Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Character of the Wicked
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.
In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;
mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;
ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”