Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Censer

8 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Kai Kora da ƙungiyarka, gobe, za ku ɗauki farantai,

  2. ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan wanda Ubangiji ya zaɓa a tsakaninmu sh ne mai tsarki. Ku Lawiyawa ku ne kuka wuce gona da iri!”

  3. Musa ya ce wa Kora, “Da kai da kuma dukan ƙungiyarka za ku bayyana a gaban Ubangiji gobe, kai da su. Haruna ma zai kasance a can.

  4. Kowannenku zai ɗauki faranti yă zuba turare a ciki. Wato, farantai 250 ke nan, a kuma miƙa su a gaban Ubangiji. Kai da Haruna za ku miƙa farantanku, ku ma.”

  5. Sai kowane mutum ya ɗauki farantinsa, ya sa wuta da kuma turare a ciki, suka tsaya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada.

  6. “Ka gaya wa Eleyazar ɗan Haruna, firist, yă kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, yă watsar da gawayin a wani wuri, gama farantan tsarkakakku ne,

  7. gama an yi amfani da farantan don miƙa mini turare. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo musu mutuwa ka ƙera farantan, ka yi murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, suka zama tsarkakakku. Bari su zama alama ga Isra’ilawa.”

  8. Haka Eleyazar, firist, ya tattara farantan tagulla waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo, ya ƙera murfin bagade da su,