Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Caldron

11 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar haikali.

  2. Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe.

  3. Suna cewa, ‘Lokaci bai yi kusa da za a gina gidaje ba? Wannan birni yana tukunyar dahuwa, mu ne kuwa naman.’

  4. Saboda haka yi annabci a kansu; yi annabci, ɗan mutum.”

  5. Sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya kuma faɗa mini in ce, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, haka kuke cewa, ya gidan Isra’ila, amma na san abin da yake a zuciyarku.

  6. Kun kashe mutane da yawa a wannan birni kuka kuma cika titunanta da gawawwaki.

  7. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa gawawwakin da kuka zubar a can su ne naman, wannan birni kuwa ita ce tukunya, amma zan kore ku daga cikinta.

  8. Kuna jin tsoron takobi, kuma takobi ne zan kawo muku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  9. Zan kore ku daga birnin in miƙa ku a hannuwan baƙi in kuma azabtar da ku.

  10. Za ku mutu ta wurin takobi, zan kuma hukunta ku a iyakokin Isra’ila. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.

  11. Wannan birni ba za tă zama muku tukunya ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinta ba; zan hukunta ku a iyakokin Isra’ila.