Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Booth

6 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A rana ta fari, za ku ɗebi zaɓaɓɓun ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, da rassan dabino, rassa masu ganye, da kuma ganyayen itacen wardi na rafi, ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, kwana bakwai.

  2. Za ku kiyaye bikin nan har kwana bakwai a kowace shekara ga Ubangiji. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsarraraki masu zuwa, ku kiyaye ta a wata na bakwai.

  3. Ku zauna a bukkoki kwana bakwai. Dukan ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa, za su zauna a bukkoki

  4. don zuriyarku tă san cewa na sa Isra’ilawa suka zauna a bukkoki sa’ad da na fitar da su daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  5. kuma cewa ya kamata su yi shelar wannan magana, su kuma yaɗa ta a duk garuruwansu da kuma cikin Urushalima cewa, “Ku fita zuwa cikin ƙasar tudu ku kawo rassa daga itatuwan zaitun da na zaitun jeji, da kuma daga dargaza, da dabino da itatuwa masu ganye, don yin bukkoki”, kamar yadda yake a rubuce.

  6. Sai mutanen suka fita suka dawo da rassa suka kuma yi wa kansu bukkoki a bisa rufin ɗakunansu, a cikin filaye, a shirayin gidan Allah, da ciki dandalin da yake kusa da Ƙofar Ruwa, da kuma a dandalin da yake a Ƙofar Efraim.