Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Anthropomorphisms: Miscellaneous figures

8 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Miscellaneous figures

  1. Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa.

  2. Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.

  3. Sai Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin yi?

  4. Lalle Ibrahim zai zama al’umma mai girma da kuma mai iko, kuma ta wurinsa dukan al’umman duniya za su sami albarka.

  5. Saboda na zaɓe shi don yă umarci ’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.”

  6. Ta Dawuda. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.

  7. Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni.

  8. Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.”