Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Anointing of the Holy Spirit

7 ayoyi · 8 fannoni

Nemi "Anointing of the Holy Spirit"

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.

  2. Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi.

  3. Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.”

  4. Na sami Dawuda bawana; da mai na mai tsarki na shafe shi.

  5. Hannuna zai kasance tare da shi; tabbatacce hannuna zai ƙarfafa shi.

  6. Babu abokin gāban da zai sa yă biya haraji; babu mugun mutumin da zai danne shi.

  7. Zan murƙushe maƙiyansa a gabansa in kashe dukan abokan gābansa.