Skip to content

Zabura98

Nasarar Allah da ceton dukan duniya

1
Zabura ce. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto.
2
Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.
3
Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.

Kira ga dukan duniya su yabi Allah su yi masa sujada

4
Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
5
ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa,
6
tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.

Halitta tana jiran hukuncin Sarki

7
Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta.
8
Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki;
9
bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options