Skip to content

Zabura79

1
Zabura ta Asaf. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai.
2
Sun ba da gawawwakin bayinka kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama, nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya.
3
Sun zubar da jini kamar ruwa ko’ina a Urushalima, kuma babu wani da zai binne matattu.
4
Mun zama abin reni ga maƙwabta, abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
5
Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne? Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta?
6
Ka zuba fushinka a kan al’umman da ba su yarda da kai ba, a kan mulkokin da ba sa kira bisa sunanka;
7
gama sun cinye Yaƙub suka lalatar da ƙasar zamansa.
8
Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu; bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu, gama mun fid da zuciya sarai.
9
Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, saboda ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu saboda sunanka.
10
Don me al’ummai za su ce, “Ina Allahnsu yake?” A idanunmu, ka sanar wa al’ummai cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar.
11
Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka; ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa.
12
Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji.
13
Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka, za mu yabe ka har abada; daga tsara zuwa tsara za mu yi ta ba da labarin yabonka.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options