Tsallake zuwa abun ciki

Zabura67

Addu’ar neman albarka da hasken Allah

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela
2
don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.

Kira ga al’ummai su yabi Allah

3
Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.
4
Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela
5
Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.

Amfanin albarkar Allah

6
Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.
7
Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options