Skip to content

Zabura54

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?” Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.
2
Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina.
3
Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela
4
Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.
5
Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su.
6
Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.
7
Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options