Skip to content

Zabura46

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
2
Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
3
ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela
4
Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.
5
Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe.
6
Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.
7
Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela
8
Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya.
9
Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta.
10
“Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.”
11
Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options