Skip to content
Zakariya 9:1-8

Zakariya 9:1-8

1
Annabci. Maganar Ubangiji tana gāba da ƙasar Hadrak za tă kuma sauko a kan Damaskus, gama idanun dukan mutane da na kabilan Isra’ila suna a kan Ubangiji,
2
da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita, da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai.
3
Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi; ta tara azurfa kamar ƙasa, zinariya kuma kamar tarin shara a tituna.
4
Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta, zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku, wuta kuma za tă cinye ta.
5
Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro; Gaza za tă yi birgima cikin azaba, haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya. Gaza za tă rasa sarkinta za a kuma gudu a bar Ashkelon.
6
Baƙi za su mallaki Ashdod, kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa.
7
Zan kawar da jini daga bakinsu, zan kuma cire abincin da aka haramta daga tsakanin haƙoransu. Waɗanda za a bari za su zama na Allahnmu, su kuma zama shugabanni a Yahuda, Ekron kuma za tă zama kamar Yebusiyawa.
8
Amma zan kāre gidana daga sojoji masu kai da kawowa. Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba, gama yanzu ina tsaro.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options