Skip to content
Zakariya 12:10-14

Zakariya 12:10-14

10
“Zan kuma zubo wa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima ruhun alheri da na addu’a. Za su dube ni, wannan da suka soke shi, za su kuma yi makoki dominsa kamar yadda mutum yakan yi makokin mutuwar ɗansa tilo, su kuma yi baƙin ciki ƙwarai kamar yadda mutum yakan yi baƙin ciki don ɗan fari.
11
A ranan nan kuka a Urushalima zai yi yawa kamar kukan Hadad Rimmon a filin Megiddo.
12
Ƙasar za tă yi makoki, kowane iyali zai yi makoki a ware, tare da matansu su ma a ware, iyalin gidan Dawuda da matansu, iyalin gidan Natan da matansu,
13
iyalin gidan Lawi da matansu, iyalin gidan Shimeyi da matansu,
14
dukan sauran iyalan kuma da matansu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options