Hoppa till innehåll
Zakariya 1:13-17

Zakariya 1:13-17

13
Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa.
14
Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona,
15
amma ina fushi da ƙasashen da suke ji suna zaman lafiya, na ɗan yi fushina kawai, amma sai suka ƙara musu masifar.’
16
“Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
17
“Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options