Titus 1:1-4
1
Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah
2
duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,
3
da lokacin da Allah ya zaɓa ya cika sai ya bayyana maganarsa a sarari ta wurin wa’azin da aka danƙa mini amana ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu,
4
Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya. Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu, su kasance tare da kai.
Settings