Waƙar Waƙoƙi 6:4-7
4
Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.
5
Ki kau da idanu daga gare ni; gama suna rinjayata. Gashinki yana kama da garken awakin da suke gangarawa daga Gileyad.
6
Haƙoranki suna kama da garken tumakin da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai.
7
Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.
Settings