Waƙar Waƙoƙi 5:10-16
10
Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma, da ƙyar a sami irinsa ɗaya a cikin dubu goma.
11
Kansa zinariya ce zalla; gashinsa dogaye ne baƙi wuluk kamar hankaka.
12
Idanunsa sun yi kamar na kurciyoyin da suke kusa da ruwan rafi, da aka wanke da madara aka kuma kafa kamar kayan ado masu daraja.
13
Kumatunsa kamar lambun kayan yaji suna ba da turare. Leɓunansa sun yi kamar furen bi-rana suna ɗiga da mur.
14
Hannuwansa kamar sandunan zinariyar da aka sa musu duwatsu masu daraja. Jikinsa ya yi kamar gogaggen hauren giwan da aka yi masa ado da duwatsun saffaya.
15
Ƙafafunsa sun yi kamar ginshiƙan dutsen alabastar da aka kafa su a cikin rammukar zinariya. Kamanninsa ya yi kamar Lebanon, mafi kyau kamar itacen al’ul nasa.
16
Bakinsa zaƙi ne kansa; komensa yana da kyau. Haka ƙaunataccena, abokina, yake ’yan matan Urushalima.
Settings