Waƙar Waƙoƙi 4:12-16
12
Ke lambu ne da aka kulle, ’yar’uwata, amaryata; ke maɓulɓula ce da aka kewaye, maɓulɓular da aka rufe.
13
Shuke-shukenki gonar rumman ne da ’ya’yan itace masu kyau na lalle da nardi,
14
nardi, da asfaran, kalamus, da kirfa, da kowane irin itacen turare, da mur da aloyes da kuma dukan kayan yaji masu kyau.
15
Ke lambun maɓulɓula ne, rijiya mai ruwan da yake gudu yana gangarawa daga Lebanon.
16
Farka, iskar arewa, ki kuma zo, iskar kudu! Hura a kan lambuna, don ƙanshinsa yă bazu har waje. Bari ƙaunataccena yă zo cikin lambunsa yă ɗanɗana ’ya’yan itacensa mafi kyau.
Settings