Skip to content
Rut 2:1-10

Rut 2:1-10

1
To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz.
2
Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.” Na’omi ta ce mata, “Ki je, ’yata.”
3
Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek.
4
Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “Ubangiji yă kasance tare da ku!” Sai suka amsa, “Ubangiji yă albarkace ka!”
5
Sai Bowaz ya tambayi shugaban masu girbinsa, “Wace yarinya ce wannan?”
6
Shugaban ya amsa, “Ita ce mutuniyar Mowab da ta zo daga Mowab tare da Na’omi.
7
Ta ce, ‘Ina roƙo a bar ni in bi bayan masu girbin in yi kala.’ Haka ta shiga cikin gonar ta kuwa yi aiki tun da safe har zuwa yanzu, sai ɗan hutun da ta yi kaɗan.”
8
Saboda haka Bowaz ya ce wa Rut, “’Yata, ki saurare ni. Kada ki tafi ki yi kala a wani gona, kada kuma ki tafi daga nan. Ki tsaya nan tare da ’yan matana bayi.
9
Ki lura da gonar da mutanena suke girbi, ki bi su tare da ’yan matana. Na riga na faɗa wa mazan kada su taɓa ke. Kuma duk sa’ad da kika ji ƙishirwa, ki tafi ki ɗebo ruwa daga tulunan da mazan suka cika.”
10
Jin haka, sai ta rusuna da fuskata har ƙasa ta ce, “Me ya sa na sami irin wannan tagomashi a idanunka da har ka lura da ni, ni da nake baƙuwa?”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options