Romawa 7:8-13
8
Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne.
9
Dā kam ina da rai sa’ad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu.
10
Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce.
11
Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni.
12
Saboda haka fa, dokar tana da tsarki, umarnin kuma yana da tsarki, su duka suna da adalci da kuma kyau.
13
Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa.
Settings