Skip to content
Romawa 6:12-23

Romawa 6:12-23

12
Saboda haka kada ku bar zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa yă sa ku zama masu biyayya ga mugayen sha’awace-sha’awacensa.
13
Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci.
14
Gama zunubi ba zai zama maigidanku ba, domin ba kwa ƙarƙashin doka, sai dai ƙarƙashin alheri.
15
Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan!
16
Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan?
17
Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku.
18
An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.
19
Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki.
20
Sa’ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.
21
Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne!
22
Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.
23
Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options