Romawa 4:13-16
13
Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya.
14
Gama da a ce masu kiyaye doka ne magāda, ai, da bangaskiya ba ta da amfani, alkawarin kuma ya zama banza,
15
domin doka tana jawo fushi ne. Kuma inda babu doka babu keta umarni ke nan.
16
Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka.
Settings