Romawa 11:25-36
25
Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika.
26
Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.
27
Wannan kuwa shi ne alkawarina da su sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”
28
Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu,
29
gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa.
30
Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu,
31
haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku.
32
Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa.
33
Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace! Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike, hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!
34
“Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa yă ba shi shawara?”
35
“Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu, da Allah zai sāka masa?”
36
Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance. Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.
Settings