Ru’uya ta Yohanna 8:3-6
3
Wani mala’ika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yă miƙa tare da addu’o’in dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin.
4
Hayaƙin turaren tare da addu’o’in tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun mala’ikan.
5
Sai mala’ikan ya ɗauki kaskon, ya cika shi da wuta daga bagaden, ya kuma wurga shi bisan duniya; sai aka yi ta yin tsawa, ƙararraki, walƙiya, da kuma girgizar ƙasa.
6
Sai mala’iku bakwai ɗin nan da suke da ƙahoni bakwai suka shirya don su busa su.
Settings