Ru’uya ta Yohanna 6:1-4
1
Na kalli yayinda Ɗan Ragon ya buɗe hatimin farko na hatimai bakwai ɗin nan. Sai na ji ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai ya yi magana da murya mai kama da tsawa ya ce, “Zo!”
2
Na duba, can kuwa a gabana ga wani farin doki! Mai hawansa yana riƙe da baka, aka kuma ba shi rawani, ya yi sukuwa ya fito kamar mai nasara da ya kutsa don nasara.
3
Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na biyun, sai na ji halitta mai rai na biyu ya ce, “Zo!”
4
Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yă ɗauke salama daga duniya yă kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings