Ru’uya ta Yohanna 4:1-2
1
Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.”
2
Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa.
Settings